27 Yuli 2014 - 18:09
Isra’ila zata ci gaba da kai hari a Gaza-Netanyahu

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya zargi Hamas da keta yarjejeniyar tsagaita wuta ta wuccin gadi da suka amince yana mai shan alwashin cewa Isra’ila zata ci gaba da kai farmaki a Gaza domin kare Yahudawa.

A yau Lahadi Kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa’o’I 24, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bukata. Amma Netanyahu ya yi watsi da kiran a tsagaita wutar bayan wa’adin ta sa’o’I 12 ta kawo karshe.

Mr. Natenyahu ya shaidawa kafar telebijin ta CNN cewa Hamas ta karya yarjejeniyar da ta amince don haka Isra’ila zata dauki matakan da suka dace domin kare mutanenta.

Falasdianwa sama da 1,000 aka kashe tun ranar 8 ga watan Yuli da Isra’ila ta kaddamar a hare hare a Zirin Gaza. Sojin Isra’ila kuma kimanin 43 ne suka mutu a hare haren da Hamas. ABNA